Yaya Toure Ya Bada Sanarwar Yin Murabus Daga Takawa Kasar Sa Leda

A yau Talata ne shahararren dan wasan kwallon kafa dan kasar Ivory Coast me takawa kungiyar kwallon kafa ta Manchester City wasa wato Yaya Toure, ya bayyana muradinsa na yin murabus daga buga wasan kwallon kafa na kasa kasa da kasashen yammacin Afirka.

Toure ya lashe kofin kasashen nahiyar Afirka AFCON a kungiyar kwallon kafa ta Elephant a shekarar 2015.

Dan wasan mai shekaru 33 da haihuwa wanda ya taka wa kasar sa rawar gani a wasannin kwallon kafa ya bar wa masoyansa wani layi ne a shafinsa na Twitter inda ya bar bayanan aje takalman nasa.

A bayanan nasa ya bayyana cewa “akwai matukar wahalar yanke hukuncin yin hakan, amma ya zama wajibi in ba masu tasowa wuri”

Ya kara da cewa “bayan na kwashe shekaru goma sha hudu da kungiyar kwallon kafa ta kasar Ivory Coast Elephant, yau na zo karshen bugawa kasar wasa”.