Babban abin shi’awa a ire-iren sana’oin dogaro da kai da muke koyawa ‘yan mata bayan an tashi daga makaranta, ya sa sun zamo masu dogaro da kai ta hanyar kashe wa kansu kananan bukatu inji wata malamar Makaranta, Malama Safiya Muhammad Lawal.
Malama Safiya, ta kara da cewa daga cikin abinda ke ci musu tuwo a kwarya dai shine yadda a makarantar da take koyarwa a mafi yawan lokuta matan kan hakura da ci gaba da neman ilimi da zarar sun yi aure.
Bayan wani lokaci kuma da zarar an sami matsala da lamarin auren sai su dawo makaranta, hakan na dawo da harkar karatun nasu baya inji malama Safiya.
Ta kara da cewa ta sami damar karantar kwas din da take koyawa ‘yan matan ne a jami’a, duk da cewa a lokacin da take karatun, ta rasa iyayenta hakkan dai bai sa ta yi kasa a gwiwa ba da lamarin karatun ta ba duk kuwa da ire-iren kalubalen da ke tattare da rashin iyaye
Daga karshe ta bayyana cewa tana karatu a hannu guda tana sana’oin da suka danganci saka, dinka hijabi da ma koyar da hada sabulun wanka da na wanki.
Your browser doesn’t support HTML5