Ganin yadda muhimman mutane ke kara ziyartar Najeriya, wanda na baya-bayan nan shi ne Sakatare-Janar din Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, wani kwararre ya lura cewa saboda saukin sadarwa da fasahar zamani ta kawo, wanda ya maida duniya tamkar dunkulalliyar kasa – abin da ake kira “Globalization” da Turanci, babu kasar da za ta iya kasancewa ita kadai ta gamsu ta fuskar tattalin arziki da lafiya da sufuri da dai sauran harkokin dan adam.
A cewar mai tsokaci kan harkokin yau da kullum kuma malami a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna (Kadpoly) mai suna Isyaku Alhassan Kauran Mata a hirarsu da abokin aikinmu Usman Kabara, ziyarar wata alama ce cewa duniya na kara amincewa da Najeriya. Ya kara da cewa kusan kowace kasa na rabe ne da wata ta huldar kasa da kasa.
Ya ce hasalima, idan kasa ta karbu a duniya, irin wadannan ziyarce-ziyarcen kan karu sosai kuma hakan na da fa’ida saboda ta haka ne masu sha’awar saka jari ta fannoni dabandaban za su ga irin sassan da za su saka jari ko kafa masana’antu. Ya ce shi ya sa ma idan aka ware kasa sai ta tsiyace. Ya ba da misali da zamanin Abacha lokacin da, in ji shi, kasashen duniya da dama su ka maida Najeriya saniyar ware, amma Abacha na mutuwa sai al’amari ya canza; aka rinka shigo Najeriya akai-akai; su ma jami’an Najeriya su ka sami sukunin ziyartar kasashe dabandaban ta yadda mai sha’awar zuba jari ke iya zuwa hakanan ma mai sha’awar yawon bude ido. Kauran Mata ya ce haka ma wannan gwamnatin ta Muhammadu Buhari ta samu karbuwa ta yadda kasashe da daidaikun mutane ke ganin da alamar kwanciyar hankali zai wadata har a iya saka jari sosai da sauran harkokin da ba a iya yi cikin tashin hankali.
Your browser doesn’t support HTML5