Yawan Mata a Fagen Siyasar Najeriya Ya Ragu

'Yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyin su akan rawar da mata ke takawa a fagen siyasar kasar.

Adadin mata a gwamnatin Najeriya a cikin shekaru 3 da suka gabata ya ragu zuwa kashi shida kuma babbar ‘yar takarar shugaban kasa a Najeriya, Oby Ezekwesili, ta janye daga takarar.

Mrs. Oby Ezekwesili ta kudiri aniyar kawo sauyi a fagen siyasar Najeriya a lokacin da ta tsaya takarar neman zama mace ta farko a matsayin shugabar kasa.

Amma sai ta janye daga takara makonni 3 kafin zaben na ranar 16 ga watan Fabarairu don ta hada hannu da hadakar jam’iyyun adawa don ganin an kawar da manyan jam’iyyun siyasar kasar.

Wannan matakin ya ba masu goyon bayanta irin su Raymond Chinedu mamaki, wanda ke ganin ta a matsayin wadda zata kawo daidaito tsakanin jinsuna.

Raymond “Yace a Najeriya, da wuya a taimakawa mace har zuwa wannan matakin, kaji inda aka sami karayar gwiwar amma mun yi imanin cewa idan mazan sun gaza a tsawon wannan lokacin, tunanin mu shi ne akalla idan aka sami mace a gwamnati, dake jagorancin gwamnatin, mun yi imanin ta yiwu a sami sauyi.

Hukumar zaben Najeriya ta INEC ta ce kashi 6 kacal na mukaman siyasa mata suka mallaka a kasar. Darakta Oluwole Osaza, ya dora laifin karancin mata a fagen siyasa akan bambance bambancen ala’ada da addini.

Osaze ya ce “kasar Rwanda na da yawan mata da suka fi na Najeriya. Daya daga cikin dalilan shi ne matakan da aka dauka a kasar, saboda a dokokin su, su na da wadannan. Mu kuma bamu da su.

Rahoton Timothy Abiezu.