Yau Za a Fara Gasar UEFA Na Bana

UEFA

A yau talata 12 ga watan Satumba shekara dubu biyu da sha bakwai, za'a fara buga gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, na shekara 2017/18 (UEFA Champions League) karo na 63,

Kungiyoyin kwallon kafa talatin da biyu 32, daga kasashe daban daban dake yankin Turai zasu fafata a tsakaninsu domin fidda zakara a bana, a bisa tsarin rukuni takwas.

A shekarar da ta gabata 2016/17 kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, dake kasar Spain ita ta lashe gasar, akan kungiyar kwallon kafa ta Juventus na Italy.

Kuma itace kungiyar da tafi kowace kungiya daukar kofin a duniya, tun bayan da aka fara a shekaru 62, da suka wuce.

Real Madrid, dai ta dauka sau Goma sha biyu 12, Za'a kuma fara wasan na yaune a matakin wasan rukuni rukuni.

Barcelona da Juventus, Roma da Atletico Madrid, Manchester United da Basel, Celtic da PSG, Chelsea da Qarabag, Bayern Munich da Anderlecht, Olympiacos da Sporting CP, Benfica da CSKA Moscow,

Za'a fafata wasannin ne dukka da misalin karfe takwas saura kwata na dare agogon Najeriya,Nijar, Kamaru, da Kasar Chadi.

Your browser doesn’t support HTML5

Yau Za a Fara Gasar UEFA Na Bana - 2'57"