Yau Za'a Fara Gasar Cin Kofin 'Yan-Mata Na Duniya

A yaune za'a fara gasar cin kofin kwallon kafar mata na duniya na 2019 a Kasar Faransa. A shekara ta 2015 ne dai kasar Faransar ta samu damar daukar nauyin gasar wanda za'ayi a birane Tara na kasar.

Ingila da Scotland na daga cikin kasashe 24 da za'a fafata dasu a gasar, kuma zasu kara da juna a rukunin D a ranar Lahadin nan. Ita kuwa mai masaukin baki Faransa, za ta taka leda ne da Koriya ta Kudu a filin wasa na Parc des Princes a wasan farko da za'a buga yau din nan.

Mai rike da kambun gasar wato Amurka za tayi fito na fito ne da Thailand a ranar Talatatar nan 11 ga watan Yuni.

Ga yadda jadawalin wasan yake: A rukunin A akwai: Faransa, Koriya ta kudu, Norway da kuma Najeriya. Rukunin B ya kunshi China, Jamus, Afrika ta Kudu da kuma Spaniya.

A rukunin C kuwa akwai Australia, Brazil, Italiya da Jamaica. Rukunin D ya hada da Argentina, Ingila, Japan da Scotland. Rukunin E akwai kasashen Kamaru, Canada, Netherlands da kuma New Zealand.

Rukunin F kuma wanda shine na karshe ya kunshi Chile, Sweden, Thailand da Amurka.

Wasan wanda za'a fara a wannan Jumma'ar 7 ga wata Yuni, a kammala wasan a ranar Lahadi 7, ga watan Yuli. Shine karon farko da za'ayi amfani da na'urar Video tallafawa Alkalin wasa wato (VAR).