Tsohon zakaran wasan kwallon kafa, George Weah, dan shekara 51 da haihuwa, ya zama sabon shugaban Liberiya bayan da aka rantsar da shi yau Litinin a wani biki da aka yi a katafaren filin wasan dake babban birnin kasar Monrovia wanda ya cika makil da jama'a.
Shugabannin kasashen Gabon, Ghana da Saliyo suka kasance wurin rantsar da George Weah.
A cikin jawabinsa sabon shugaban ya ce "Na kwashe shekaru da dama a rayuwa ta ina wasa a filayen kwallo, amma yau ina ji wani iri ne daban da babu irinsa", in ji shi. Ya yiwa shugabar kasar mai barin gado Ellen Johnson Sirleaf godiya wadda ya ce "ta gina tushen da zasu iya tsayawa kai cikin lumana".
Sabon shugaban ya yi takara ne da tsohon mataimakin shugaban kasa Joseph Boakai wanda shi ma ya sauka bayan ya yi wa'adi biyun da kundin tsarin mulkin kasar ya kayyade.
Weah ya ce abun da zai fara tinkara shi ne yaki ba sani ba sabo da cin hanci da rashawa.
Bikin na yau Litinin shi ne na farko da za'a mika mulki cikin lumana a shekaru fiye da saba'in a tarihin kasar.