Yau Talata Majalisar Dokokin Zimbabwe zata fara yunkurin tsige Shugaba Robert Mugabe

Robert Mugabe wanda yayi kunnen kashi da wa'adin da aka bashi ya sauka daga mulki

Lokacin da sojoji suka yi masa daurin talala sun bashi zarafi ya kare mutuncinsa amma shugaba Robert Mugabe ya ki, jam'iyyarsa dake mulkin kasar ta bashi wa'adi har zuwa jiya ya sauka daga mulki amma yayi kunnen shegu saboda haka yanzu majalisar kasar zata tsigeshi

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe yayi kunnen kashi da wa’adin da jam’iyyarsa mai mulki ta bashi na ya sauka daga mulki kafin tsakar ranar jiya Litinin.

A yau Talata ne ake sa ran Majalisar kasar zata fara yunkurin tsigeshi, amma yunkurin na iya ‘daukar lokaci mai tsawo da sarkakiya ko kuma ya zamanto bai yi tasiri ba.

Lovemore Madhuku, malami ne dake koyar da fannin shari’a a jami’ar Zimbabwe. Ya ce ‘daukar matakin korar shugaban zai iya zamantowa abu mai wahalar gaske, saboda ba wai kawai Majalisa ta kada kuri’a amincewa bane kadai.

“Yace idan mukace tsige shugaba a tsarin kasar Zimbabwe, hakan yana nufin yin shari’a. kana zargin shugaban kasa da aikata wani laifi, kuma kana son ayi masa shari’a akai. Idan aka same shi da laifin abin da ake zarginsa da yi, to za a iya sallamarsa daga aikinsa na shugaban kasa. Sai dai ba zaka iya yin hakan ba a rana ‘daya ba. yana daukar watanni kafin akai ga tsige shugaban.”

Kundin tsarin mulkin kasar Zimbabwe ya shimfida wasu shuruda hudu da za a iya tsige shugaban kasa akan su. Wadanda suka hada da tafka kuskure mai girma da rashin biyayya da rashin aiki da kundin tsarin mulkin kasa da kuma gaza yin aiki a matsayin shugaban kasa saboda matsalar nakasa ko gushewar hankali.