Yau kimanin Musulmi masu aikin Hajji miliyan biyu suke yin hawan Arafat, a wurin da Musulmi suka hakikanta cewa,a nan ne Annabi Muhammadu SAW ya yi hudubarsa ta karshe kimanin shekaru dubu daya da dari hudu da suka shige, inda yayi kira da a sami hadin kai da mutunta juna tsakanin al’ummar Musulmin duniya.
An fara aikin Hajjin na kwanaki biyar jiya Talata da kewaya Dakin Kaaba, daga nan masu aikin Ibadan zasu wuce zuwa Minna kafin soma hawan tsaunin Arafat.
Aikin Hajji yana cikin shika shikan Musulunci guda biyar da suka hada da gaskanta cewa Allah daya ne kuma Annabi Muhammadu SAW shine manzonsa na karshe, da yin salloli biyar a kowace rana, da kuma bada zakkah da kuma yin azumin watan Ramadan.
Hatsarin da aka yi a babban Masallacin birnin Makkah, a farkon wannan watan da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 109 da suka hada da wadansu masu aikin ibada ‘yan kasashen ketare, sanadiyar karyewar wata kugiyar daukar kayan gine-gine, bai hana Mahajjatan ayyukan ibada ba.
Kimanin mutane 400 suka ji rauni a wannan hadarin.