Yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don jaddada muhimmancin zaman lafiya tsakanin al’umma. Wakilin Muryar Amurka a birnin Ibadan, Hassan Ummaru Tambuwal ya ruwaito Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Mr. Ban Ki-moon na kira ga kasashen duniya da su hada kai wajen tabbatar da zaman lafiya tsakanin al’umma.
Wakilinmu a birnin Ibadan na jihar Oyo, Hassan Ummaru Tambuwal ya ruwaito wani mai suna Abarshi a kasuwar Shanu da ke Ibadan na cewa ya na da kyau da Majalisar Dinkin Duniayar ta ware wsannan ranar, to amma zaman lafiya bai yiwuwa muddun babu zaman adalci. Y ace yakamata a inganta asibitoci da makarantu da sauran abubuwan da talaka ke amfana da su muddun ana son hankalin jama’a ya kwanta.
Shi ma wani mai suna Abdullahi y ace fatansa shi ne a samu zaman lafiya a arewa maso gabashin Nijeriya da ma duniyar baki daya. Shi kuwa Suleiman Umar kira ya yi da cewa albarkacin wannan ranar Shugabanni su yi rungumi akidar aldalci don a zamu zaman lafiya mai dorewa.
Your browser doesn’t support HTML5