Shugaba Donald Trump zai karbi bakuncin Pirayim ministan Iraqi Haidar al-Abadi a yau Litinin don tattaunawa a kan baututuwan da ake sa ran zasu hada da farmakin da aker kaiwa na kwato birnin Mosul dake arewacin Iraqi daga hannun ‘yan kungiyar Da’esh ko ISIS.
Shugabannin biyu sun tattauna a kan batun yaki da ISIS ta waya a watan da ya gabata, amma a yau litinin ne zasu yi tattaunawarsu ta farko ido da ido.
Kafin ya baro kasarsa zuwa Washington, Abadi yace zai tattauna da shugaba Trump game da yanda za a kawo karshen kungiyar ISIS da masu basu taimako.
Dakarun Iraqi suna papatawa da mayakan yan ta’addar a kasa tare da taimakon kai farmaki ta sama daga kungiyar hadaka karkashin jagorancin Amurka wadda tun shekarar 2014 take auna yan ISIS.
Yakin sake kwato birnin Mosul ya fara ne a bara kuma kawo yanzu dakarun Iraqi sun yi nasarar kwace gabashin birnin kuma suna kutsawa a yammacin birnin.
Jirgi mai saukar ungulu na Iraqi a jiya Lahadi ya harba roka a kusa da wani babban masallaci a yammacin birnin Mosul a kokarin da rundunar kasar keyi na kaiwa wurin da shugaban kungiyar Da’esh, ko ISIS, Abu Bakr al-Baghdadi, ya ayyana kafa Daular Islama a shekarar 2014.