Ma'aikata a sassan duniya sun hau tituna Alhamis dinnan don bukukuwan zagayowar ranar Ma'aikata ta kasa da kasa da ake kuma kiranta Ranar Watan Mayu, inda su ka yi ta maci tare da kiraye kirayen a kara albashi a kuma kyautata yanayin aiki.
WASHINGTON, DC —
A birnin Istanbul na kasar Turkiyya 'yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa da ruwan zafi don tarwatsa masu zanga-zangar da ke niyya dannawa zuwa Dandalin Taksim, inda nan ne akan yi gangamin ranar ta Ma'aikata.
Bara, gagarumin gangamin ranar ta Ma'aikata ya rikide zuwa wata babbar gwagwarmayar adawa da gwamnati.
A birnin Moscow, ma'aikatan kasar Rasha sun yi maci a dandalin "Red Square" cikin yanayin bayyana son kasarsu.
Masu maci sun yi ta daga kwalaye masu dauke da sakonnin da aka rubuta cewa "Ina alfahari da kasata" da kuma "Mun fa yadda da Shugaban Kasarmu" da dai sauransu.
Rabon a yi irin wannan maci a dandalin Red Square tun a farkon 1990 da dan dori.
Hakazalika an yi gangami a sassan Asia. Dubban ma'akata da 'yan raji sun hau bisa tituna a Manila don kiran a kara albashi a daidai lokacin da abubuwa ke kara tsada.
A Cambodia, ma'aikatan masaku masu bukatar a kara masu albashi a kuma kyautata masu yanayin aiki sun yi gangami a Phnom Penh.