Yau Ranar Farko Da MDD Ta Ware Domin Bikin Karrama Mata Alkalai Ta Duniya 

Yau Ranar Farko Da MDD Ta Ware Domin Bikin Karrama Mata Alkalai Ta Duniya - Ghana

Yayin da ake bukin ranar Alkalai Mata ta Duniya, kasar Ghana ta doshi cika muradun ci gaba mai dorewa (SDG) na Majalisar Dinkin Duniya tare sa samun kashi 50 cikin 100 na yawan mata alkalai a shekarar 2030, wanda zai baiwa mata damar ba da gudunmarsu wajen tabbatar da adalci.

ACCRA, GHANA - Ranar 10 ga watan Maris, 2022 ne aka fara bikin Ranar Alkalai Mata ta Duniya, karo na farko, bayan Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana ranar a shekarar 2021, domin inganta daidaito da kuma shigar mata a matakai daban-daban na shari'a.

Taken bikin na bana shi ne, "Mata masu adalci, mata domin adalci," wato domin samun adalci, ana bukatar karin mata masu adalci.

Yau Ranar Farko Da MDD Ta Ware Domin Bikin Karrama Mata Alkalai Ta Duniya - Ghana

Lauya Anas Mohammed ya yi karin bayani game da bukin wannan rana, inda ya ce, ranar na baiwa mata wani kwarin gwiwa a kotu, domin sun san za'a yi musu adalci. Haka kuma zai sa wasu dalibai mata da suke da burin aikin lauya su kara himma, idan sun san cewa za su iya zama alkalai, ba matsayi ne na maza kawai ba.

Adadin mata a sashen shari'a ya bambanta tsakanin kasashe. Da jimawa, mata a galibin kasashe ba a ma ba su damar kada kuri’a balle su kasance a wani bangare na gwamnati. Amma, yanzu ci gaba da daukar ilimin ‘ya’ya mata da muhimmanci ya sa matan sun fara hawa wasu matsayin da a da maza ne suka mamaye.

Alkalumma da ma'aikatar shari'a ta Ghana ta fitar a shekarar 2022, wacce ta yi nazarin jinsin alkalai a kowace kotu a Ghana, na nuni da cewa fiye da kashi 42 cikin 100 na alkalan Ghana, mata ne; jumilla, Ghana na da alkalai 403 a lokacin da aka yi kididdigar, kuma daga cikinsu 170 mata ne sai 233 maza.

Yau Ranar Farko Da MDD Ta Ware Domin Bikin Karrama Mata Alkalai Ta Duniya - Ghana

Lauya Hummu Zakari da ke ofishin Antoni Janar na Ghana ta ce wannan alkalumman abin alfahari ne da ci gaba ga mata, musamman na Ghana. Ta kuma ce samun yawan wakilcin mata a kotu wani kwarin gwuiwa ne ga matan.

Ta jinjinawa alkalai mata, tare da yi musu addu’ar gudanar da aikinsu cikin adalci da tausayi.

A kasar Ghana an sami alkalin-alkalai mata guda biyu a jere. A wannan jamhuriya ta hudu, alkalin alkalai da ta fi kowa jimawa a kan kujerar mace ce, mai Shari’a Georgina Theodera Wood. Haka kuma mai Shari’a Sophia Akufo, ita ce babbar alkali ta farko a kotun kare hakkin bil adama ta Afirka.

Saurari cikakken rahoto daga Idris Abdullah Bako:

Your browser doesn’t support HTML5

Yau Ranar Farko Da MDD Ta Ware Domin Bikin Karrama Mata Alkalai Ta Duniya .MP3