Yau 24 ga watan Afirilun 2017 Firayim Ministan Nijar da dimbin tawagar ministoci da sarakunan gargajiya da gwamnan jihar Tawa da tsoffin 'yan tawaye suka yi bikin cikon shekaru 22 da rabtaba hannu tsakanin 'yan tawaye da gwamnatin Nijar da aka yi a shekarar 1995 a kasar Burkina Faso wanda ya kawo karshen tawayen Abzinawa
WASHINGTON DC —
Bikin ya wakana a garin Cintabara cikin jihar Tawa inda aka soma tawayen kusan shekaru 27 da suka gabata.
Wani dan jarida Malam Sidi Muhammad da ya kasance wurin bikin shi ya bada karin bayani. Yana mai cewa tun jiya da Firayim Ministan kasar ya iso suka soma bikin kafin su kammala yau, wadda kuma ta kasance ranar hutu a duk fadin kasar saboda bikin.
Yace an yi bikin cikin kwanciyar hankali da yadda ya kamata a yi.
Cikin abubuwan da Firayim Ministan yace sun hada da cewa babu wani banbanci tsakanin 'yan kasar saboda duk an zama tsintsiya madaurinki daya.
Ga rahoton Haruna Maman Bako da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5