Yau Ne Ranar Tarin Fuka Na Duniya

Yayin da ƙasashen duniya ke bukukuwan ranar yaƙi da tarin fuka, a tarayyar Najeriya cutar na ci gaba da halaka ɗaruruwan rayukan jama'a musamman ma a cikin yankunan karkara. Taken taron na bana shine “Kada a bar kowa a baya a yaki da tarin fuka”.

An dai ware wannan rana ce domin fadakar da al’umomin duniya illoli dama barnar da cutar tarin fuka ke yi a kowace shekara masamman ma a kasashen masu tasowa na Afirka, wanda za a maida hankali domin duba irin gudumawar da al’uma zasu iya bayarwa wajen yaki da kuma kawarda wannan kwayar cuta.

Wata likitar asibitin gwamnatin tarayya SMC dake Yola a jihar Adamawa Batule Isa Muhammad, wace tana cikin ayarin Likitoci mata dake gangamin wayar da kan al’uma akan wannan cuta tace zai yi wuya ace a kullum ba a kawo sabon mai cutar tarin fuka asibiti ba.

Ta kara da cewa ya zama wajibi a fadakar da jama’a akan mummunar aibin cutar tarin fuka domin a cewarta cutar bata da wuyar kamuwa, kuma tana mai cewa shi dai wannan cuta idan har mutun ya sha maganinsa kamar yadda likita ya umarta to ana fa warkewa ba kamar wasu cututtuka ba da sai dai ayi ta shan magani har tsawon rayuwa.

Najeriya na cikin kasashen da cutar ke ci gaba da hallaka jama’a, yayinda hukumomin a kasar ke ikirarin daukar matakai na magance cutar da kasha makudan kudade da sauran runa a kaba a yankunan karkara, koda yake bincike na nini da cewa abiranai ana samun nasarar yaki da cutar.

Your browser doesn’t support HTML5

Yan Ne Ranar Tarin Fuka Na Duniya - 3'53"