‘Yau Najeriya Ke Gudanar Da Bikin Ranar Tunawa Da Mazan Jiya

Shugabanin jami'an tsaron Najeriya yayin bikin tunawa da mazan jiya a Abuja

Daga 1 zuwa 15 ga Janairun kowace shekara, gwamnatin Najeriya, kama da ga matakin tarayya har zuwa jihohi, sukan gudanar da bukukuwa na tunawa da sojojin da suka sadaukar da rayukan su wajen ganin kasar ta tsayu da kafafunta.

Najeriya ta yi tsit na wani dan lokaci domin karrama sadaukarwar sojojin da suka rasa rayukansu, yayin bikin tunawa da ‘yan mazan jiya na bana daya gudana a yau Laraba.

Shugabanin jami'an tsaron Najeriya yayin bikin tunawa da mazan jiya a Abuja

Najeriya ta cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka-saidai domin cigaba da dorewarta a matsayin dunkulalliyar kasa daruruwa koma dubban zaratan dakaru sun kwanta a kokarin kare kan iyakoki da diyaucin kasar.

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (dama) da Babban Hafsan Rundunar Sojin Najeriya, Manjo Janar Olufemi Oluyede

Bikin Ranar Tunawa Da Mazan Jiya

Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ne ya wakilci Shugaba Bola Tinubu wanda ke halartar taron cigaba mai dorewa a birnin Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa, a bikin.

Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima

Baya ga Kashim Shettima, sauran mambobin majalisar ministocin Tinubu sun halarci bikin domin karrama dakarun da suka kwanta dama da iyalansu ta hanyar dora furan kallo, da gudanar da sauran al’adun soja ciki harda harba bindigogi sama.

Bikin Ranar Tunawa Da Mazan Jiya

Kowacce ranar 15 ga watan Janairu, rana ce da gwamnatin Najeriya ke gudanar da gangami na musamman don tunawa da tarin sojojin da suka rasa rayukansu a fagen yaki, ranar da ake yiwa lakabi da ranar tunawa da ‘yan mazan jiya wato Armed Forces Remembrance Day.

Bikin Ranar Tunawa Da Mazan Jiya