Daya daga cikin irin kwamitocin da gwamnatin Shugaba Buhari ta kafa, wato kwamitin yawalta shinkafa da alkama a kasar yayi taron sanin inda aka kwana da mukaddashin shugaban kasa Farfasa Yemi Osinbajo a fadar shugaban kasa yau a Abuja.
Wadanda suka halarci taron sun hada da gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele da gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da gwamnan jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar da gwamnan jihar Kebbi Alhaji Atiku Bagudu.
Sauran wadanda suka kasance a taron sun hada da Mr. Ade Ipaye na ofishin shugaban kasa da Chief Audu Ogbe ministan harkokin noma da Kemi Adeosun ministar kudi da karamin minista a ma'aikatar gona Heineken Lokpori da kuma gwamnan jihar Ebonyi David Umahi wanda jiharsa na cikin jihohin da aka kebe domin shuka shinkafa saboda mutanen Abakalili an dade da saninsu da shuka shinkafa tare da sarafata.
Akwai kuma Ambassador Yemi Dipeolu mai ba shugaban kasa shawara ta musamman akan harkokin tattalin arziki a wannan taron da aka yi a ofishin mataimakin shugaban kasa dake fadar shugaban kasa ta Aso Rock.
Taron ya maida hankali ne akan nasarar da aka cimma kawo yanzu wajen shuka shinkafa da alkama a jihohin Kebbi, Kano da Jigawa da Ebonyi da dai sauransu.
Nan da dan lokaci kasar zata wadata da shinkafa da alkama har ma ti soma fitar dasu zuwa wasu kasashen.