Kwamitin Majalisar Dattawan Najeriya da ta kafa a karkashin shugabancin Senata Aliyu Magatakardan Wamako domin ya binciki badakalar da ake zargin an tafka a kamfanin NNPC zai fara zamansa yau
WASHINGTON DC —
Shugaban kwamitin binciken, Senata Aliyu Magatakardan Wammako, a zantawar da yayi da wakilinmu Saleh Shehu Ashaka ya bayyana hakan.
Shugaban kwamitin yace, a zamansu na yau ne zasu tantance tsarin aikin da aka basu da kuma yadda zasu gudanar da shi.
Dangane da cewa ko an kafa kwamitin din ne domin a ci wa wasu zarafi, Senata Aliyu yace ba za’a yi anfani dasu ba a muzgunawa wani,zasu yi aikin ne tsakaninsu da Allah, ta yadda zasu taimakawa Shugaba Muhammad Buhari a yakin da yake yi da cin hanci da rashawa.
Ga rahoton Saleh Ashaka da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5