Yau Kungiyar Hadin Kasashen Afirka Zata Bude Taronta A Addis Ababa

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe, shugaban da ya fi dadewa kan mulki kuma ya fi kowane shugaban kasar Afirka yawan shekaru a duniya

Yau Litinin ake sa ran bude taron koli na kungiyar hada kan kasashen Afirkako AU a helkwatar kungiyar dake Addis Ababa kasar Ethiopia ko Habasha. Taken taron na bana shine "amfani da albarkar da Allah Ya yiwa nahiyar ta banbance banbancenmu ta wajen zuba jari kan matasa.

Wannan taron ne karo na farko da sabon shugaban Gambia Adama Barrow zai halarta, bada jumawa ba bayan nasara da ya samu a zaben da kuma dagar da suka ja da tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh wanda yayi mulkin kasar na tsawon shekaru 22. Haka nan shugaban da yafi kowa shekaru kuma dadewa kan mulki Robert Mugabe wanda yake mulkin Zimbabwe tun da ta sami 'yancin kai a 1980. Shugaba Mugabe dan shekaru 94 da haifuwa ya bada sanarwar a baya bayan nan cewa zai sake yin takara.

Jiya Lahadi shugabannin suka gana a asirce a halkwatar kungiyar. Ajandar taron na sirri shine tattaunawa kan yiwa kungiyar garambawul.

Ahalinda ake ciki kuma, ma'aikatar harkokin wajen kasar Check jiya Lahadi ta bada sanarwar cewa fito da, ko kubutar da wani mai Bishara Peter Jasek, daga fursina a Sudan shine "babban burinta."

Jiya Lahadi wata kotu a Khartoum ta yankewa Jasek hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari, bisa dalilai da lauyansa yace suka hada da da zargin "shiga kasar ba tareda visa ba, yin leken asiri, da daukar hotunan cibiyoyin sojAn kasar, ruruta rikcin rarraba kawunan jama'a da kuma wallafa labaran kariya."

A cikin watan Disemban shekara ta 2015 aka kama shi.