Yau Kasar Rasha Na Makokin Mutuwar Mutanenta A Hadarin Jirgin Sama A Masar

  • Ibrahim Garba

Tarkacen jirgin Rasha mai lambar tafiya A321, wanda ya fadi cikin tsaunukan Sinai na kasar Masar.

Yayin da ake kokarin gano dalilin faduwar jirgin saman Rasha a kasar Masar, 'yan Rasha na makokin tunawa da mutanenta a yau Lahadi

Yau Lahadi, Rasha na makokin mutuwar matafiya 217 da ma'aikatan jirgin sama 7, a hadarin jirgin sama jiya Asabar a yankin Sinai na kasar Masar.

Kusan dukkannin matafiyan Rashawa ne 'yan yawon bude ido da ke komawa St. Petersburg daga birnin Shakatawar nan na Sham el-Sheikh da ke Masar. Akwai kuma 'yan kasar Ukrain 3 cikin mamatan.

Ya zuwa yanzu masu ayyukan ceto sun zakulo gawarwaki akalla 129, da akwatunan nade sautuka biyu na black box, da ke nadar dukkannin al'amura masu nasaba da tafiyar jirgin ciki har da sadarwar tsakanin matukan jirgin. Kwararru na san ran wadannan na'urorin nade bayanan za su taimaka wajen sanin abin da ya haddasa faduwar jirgin.

Kungiyar ISIS, shiyyar Masar ta yi ikirarin kakkabo jirgin. To amma kwararru a fannin sufurin jirgin sama da na soji sun ce hakan ba shi yiwuwa. Su ka ce jirgin na tafiya ne da nisan mita 9,100 a sararin Subahana kafin ya rikito kuma ISIS ba ta da makami mai linzamin da zai iya kaiwa can.

Tuni wasu manyan kamfanonin jiragen sama na Turai - wato Air France da Luthansa - su ka dakatar da kittawa ta wannan wurin saboda kare lafiya.

Your browser doesn’t support HTML5

Mutanen Rasha Na Makokin Mutuwar Mutanensu A Hadadrin Jirgin Sama A Masar - 1'27''