Yau Janar Murtala Muhammad Ya Cika Shekaru 41 da Mutuwa

Sojojin Najeriya da Janar Murta ya jagoranta

Shekaru arba’in da daya bayan kisan marigayi shugaban Najeriya Janar Murtala Ramat Mohammed a wani yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba ranar goma sha uku ga watan FabraiRu na 1976, ‘yan kasan na juyayin rasuwarsa ta hanyar tunawa irin tubar da ya yi kokarin dora kasar a kai.

Sashin Hausa yayi hira da wani tsohon kwamishinan ‘yansanda Alhaji Hammawa Njidda Damare wanda al’amarin kisan Janar Murtala ya abku a idonsa.

Sauye sauyen da Janar Murtala ya kawo a zamanin mulkinsa kamar kaurar da fadar tarayyar Najeriya daga Ikko, kirkiro da karin jihohi bakwai inji irinsu tsohon ministan ilmi na Najeriya Alhaji Dauda Birma na daga cikin ayukan alheri da ‘yan Najeriya zasu rika tunawa da shi.

Matasa a wancan zamanin kamar Yusuf Etham da Jonah Morris Mangapila da ke karatu a manyan kwalejoji suna kallon marigayi shugaban kasa Janar Murtala A wani manzo ne na canji, dalili ma injisu da ya sa salon mulkinsa ya gamu da turjiya daga wani bangare na sojojin Najeriya.

A fagen difilomasiyya, Sanata Abubakar Gerei yana gani a zamanin Janar Murtala Najeriya da ma nahiyar Afrika baki dayanta ta samu daukaka a idon kasashen duniya.

Ga Sanusi Adamu da Karin bayanin.

Your browser doesn’t support HTML5

Yau Janar Murtala Muhammad Ya Cika Shekaru 41 da Mutuwa - 4' 15"