Alkalumman hukumar kiwon lafiya ta duniya ko WHO sun nuna mutane kimanin dubu sittin ne ke mutuwa a duk fadin duniya kowacce shekara sanadiyar cutar akasarinsu kuwa yara ne.
Duk wadanda ba'a yiwa allurar rigakafi ba idan karnuka dake dauke da cutar, wadda kuma ake kira haukar karnuka, suka ciji mutane to zasu kamu da ita.
Biyo bayan samun yawan koke koke daga wadanda karnuka suka ciza ya sa hukumomin kiwon lafiyar dabbobi da na mutum suka fito suka kaddamar da bada rigakafin cutar ga mutane da karnuka kyauta yau.
Dr. Sani Gambo daraktan ma'akatar kiwon lafiyar dabbobi dake Yamai yace a likitance idan mutum ya kamu da ciwon zangai sai ya dinga yin miyau idan kuma kare ne sai yayi ta gudu. Karen ba zai ji tsoron komi ba ko kuma ya tsaya. Cikin kwana biyu ko ukku da farawa sai karen ya mutu. Yace matsala ce ta gaske. Da zara sun sami mutum da kare ya ciza sai wurin likitan mutane.
Idan kare ya ciji mutum kamata yayi a kama karen a kai wurin likita mai kula da dabbobi inda za'a rikeshi na kwanaki goma sha biyar. Idan bai mutu ba to sai su sakeshi, wato bashi da cutar.
Likitocin kiwon lafiyar mutane sun ce da zara kare ya ciji mutum to nan take a je karban magani. Wannan ita ce hanya daya tilo ta kaucewa mutuwa daga cutar zangai.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5