Yau Faransa Zata Haramta Sanya Kayan Ninkaya Irin Na Burkina Faso

Wata da sanya kayan ninkayan da yau kasar Faransa zata haramtashi

A yau Juma’a a ke sa ran babbar kotun kasar Faransa za ta yanke hukuncin haramata sanya kayan yin ninkaya na Burkini da mata musulmi ke sakawa a kasar, ko kuma akasin hakan, lamarin da ya janyo cecekuce.

Zaman kotun wanda za a yi shi da rana zai shafi wasu garuruwan Faransa guda 30.

Garuruwa da dama da ke gabar tekun kasar, sun haramta sanya wannan nau’in kaya mai zubin hijabi da mata musulmi ke sakawa yayin da su ke yin ninkakyaa gabar teku.

Yunkurin haramta sanya wannan kaya ya biyo bayan korafi da Faransawa da dama suka nuna, bayan hare-haren da mayakan IS suka kai a Paris da Nice da sauran wurare cikin watanni 20 da suka gabata.

Kungiyar nan mai kare hakkin bil adama ta French Human Rights League ta soki wannan yunkuri na haramta sanya Burkini, domin a cewarta, mata suna da zabin su saka duk irin kayan da su ke so a bakin gabar tekunan Faransa.

Binciken jin ra’ayin jama’a ya nuna cewa da yawa daga cikin Faransawa, suna goyon bayan wannan yunkuri na haramta sanya Burkinin.