Kidigdigar da hukumar yawon bude ido ta yi ya nuna bangaren yawon bude ido ya samar da kudaden shiga har dalar Amurka tiriliyon daya da rabi a shekarar bara kawai.
Ana harsashen kudaden da ake samu zasu cigaba da karuwa musamman ma idan an samu zaman lafiya a kasashe daban daban.
Bikin na bana ya zo ne a lokacin da kasashe irinsu Najeriya ke fama da tabarbarewar tattalin arziki lamarin da ya sa kasar tana neman hanyoyin fita daga wannan kangin karyewar tattalin arziki.
Kasa kamar irin Najeriya na neman samun hanyoyin kara samun kudin shiga a maimakon cigaba da dogaro ga man fetur da kasar ta dogara dashi shekara da shekaru..
Wani mai kamfanin yawon bude idanu a Legas Mr. Kunle Adeyemi yace bangaren yawon bude idanu na kawo kudaden shiga kuma lokaci ya yi da ya kamata kasar ta maida hankalin akan wannan hanyar kodayake akwai kalubale. Yace banda kudaden shiga yawon bude ido na samar da ayyukan yi.
Najeriya ta mallaki wuraren yawon bude kama daga arewacin kasar zuwa kudanci da gabashin da yammacin kasar amma ba'a kula dasu ba balantana a tallatar dasu.
To saidai duk da dimbin wuraren yawon shakatawa da bude ido da kasar ke dasu yawancin 'yan Najeriya na ganin al'ada ce ta masu hannu da shuni da kuma mutanen kasashen turawa. Talakawa dake neman na yau da kullum yawon bude ido bai damesu ba.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5