Ranar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Duniya

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres.

Majalisar Dinkin Duniya ta kebe kowace ranar goma sha uku ta watan Disamba a matsayin ranar tunawa da yaki da cin hanci da rashawa ta duniya.

Ranar goma sha uku ta kowace watan Disamba, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin yaki da cin hanci da rashawa a duniya. Akan wannan ranar ce, wani Malamin Jami'ar Jihar Sokoto Farfesa Bello Bada ya yiwa Muryar Amurka bayani kan illar cin hanci da rashawa.

A cewarsa, cin hanci da rashawa na gurbata aiki. Sai kuma talauci ya biyo baya tare da haddasa rashin zama lafiya. Cin hanci yana haifar da rashin amincewa da juna. Ya kara da cewa, duk al'ummar da cin hanci ya yiwa katutu tana tare da ciwon da ba ya warkewa.

Farfesa Bello ya tabbatar da cewa, cin hanci yana da illa ga kowa, kama daga kan gwamnati da attajirai da ma talakawa. Misali idan akwai cin hanci a gwamnati, Malamin yace, idan gwamnati ta yi kasafin kudi, yawancin kudin za su kare a hannun mutane ne ba tare da sun kai ga yin aikin da ya kamata su isa ayi ba. Su kuma talakawa za su ji an yi kasafin kudi mai dimbin yawa amma ba za su gani a kasa ba.

Bugu da kari talakawa sai sun tara kudi sun kaiwa ma'aikatan gwamnati kafin ayi masu ayyukan da gwamnati tace za ta yi na jin dadinsu. Akan matakan da ya kamata gwamnati ta dauka domin kawar da cin hanci da rashawa, Farfesa Bada yace, kowace kasa na da nata tsarin. Kasashen da suka ci gaba ba su barin mutum ya ga tsabar kudi da idanunsa.

Duk abin da za su yi sai ta hanyar amfani da banki kadai. Muddin kuma aka saci kudi suna bin sawu su kama duk wadanda suke da hannu a cikin lamarin. A cewar Farfesan, idan kasa bata da doka ko kuma bata bari doka ta yi aiki ba, to kowa zai yi abinda ya ga dama ne.

A kasashe masu tasowa kamar Najeriya, ba sa bin dokoki, sannan wasu lokuta yace da bankunan ake hada baki a cuci kasar. Yace wajibi ne gwamnati ta tashi tsaye ba sani ba sabo don a yaki da cin hanci da rashawa.

A wajen yaki da cin hanci babu batun danuwantaka, acewar Farfesa Bada. Idan kuma gwamnati ba ta yi hakan ba za'a samu rudani, tashin hankali da rashin ci gaba, da rashin jin dadin jama'a tare da rashin tsaro.

Malamin ya karkare da cewa, talakawa ne ke da babbar rawar da za su iya takawa, domin sune suke tare da mutane. Sun san gwargwadon karfin mutum. Misali idan sun zabi mutum ya je majalisa, cikin shekaru biyu ya yi kazamin kudi, ya kamata su tashi su nemi sanin ta yadda ya samu arzikinsa.

Haka ma idan ma'aikacin gwamnati ne ya kudance, su bincika, su bi sawu. Idan talakawa suna tona asirin mutane, suna kyamarsu da arzikinsu, za'a samu canji.

Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ranar Yaki da Cin Hanci da Rashawa Ta Duniya - 3' 12"