A rana itin ta yau ce Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin fadakar da jama'a da kuma tara taimakon magunguna da kudade saboda tallafawa wadanda suka kamu da kwayar a duk fadin duniya.
Yau fiye da shekaru goma ke nan da majalisar ta ware wannan rana ta musamman.
A duk shekara masu dauke da cutar sukan taru wuri guda saboda fadakar da kawunan jama'a game da illolin dake tattare da cutar da kuma hanyoyin da za'a bi domin kare kai daga kamuwa da cutar..
Tun jiya aka fara taruruka akan cutar a jihar Borno inda mutane da dama dake dauke da cutar suka shirya fadakarwar..
Alhaji Musa Liman babban sakatare a hukumar dake yaki da cutar ta jihar Borno yace babban mahimmancin fadakar da mutane shi ne a san menene hukumar ta yi ko ta keyi kuma menen zata yi.
A jihar Borno an samu cigaba a yaki da cutar duk da matsalar tsaron da jihar ta samu kanta a ciki. Alkalumma da hukumar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya ta fitar a shekarar 2013 kusan mutane 5.8 cikin dari ne suke dauke da cutar a jihar amma yanzu abun ya sauka zuwa 2.4 cikin dari.
Amma a sansanin 'yan gudun hijira an samu karuwar mutane da suka kamu da cutar.
Malam Hassan Mustapha shugaban masu dauke da cutar yace ranar tana da mahimmanci gare su. Su na tunawa da wadanda suka mutu sanadiyar cutar. A ranar su kan duba baya su ga menene gwamnati ta yi masu. Na uku sukan duba irin tasirin da hukumar kiwon lafiya (WHO) ta duniya ta yi dangane da samun maganin da zai warkar dasu.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5