Yau Ce Ranar Nakasassu a Jamhuriyar Nijar

NAKASASSU

Yau ce gwamnatin jamhuriyar Nijar ta kebe domin tunawa da nakasassun kasar da yawansu ya kai 715, 475 da akasarinsu matasa ne. Saidai duk da kokarin basu ilimi yawancin iyayensu sun gwamnace su sasu yin barace barace.

Yau ake bikin tunawa da nakasassu a duk fadin Jamhuriyar Nijar da aka ba taken "kowa ya kawo nasa kokari domin baiwa nakasassu damar samun ilimi ta hanyar zuwa makaranta".

Ministar dake kula da raya al'ummar kasar ce tayi jawabi a madadin gwamnati. Tana mai cewa albarkacin kidigdiga ta shekarar 2012 da kasar ta shirya an gano akwai mutane 715, 475 nakasassu a duk fadin kasar kuma kashi 60 cikin dari shekarunsu basu kai ishirin ba. Mafi yawancin nakasassun matasa ne.

Ministar ta lura cewa gwamnatin kasar ta rabtaba hannu cikin yarjejeniyar kasa da kasa da ta ba nakasassu kariya da damar samun ilimi.

Amma Malam Nasiru Jibo shugaban makarantar makafi dake Birnin Konni yace iyayen sun fi son su sasu yin barace barace maimakon su kaisu makarantar boko.

Haka ma wani malami wanda shi ma makaho ne dake koyaswa a makarantar ya ce akwai matsaloli da dama da suka jibanci makarantar saboda lokacin da aka kafa makarantar an yi zaton daliban daga Birnin Konni da kewaye ne kawai zasu fito. Baicin hakan iyayen na bukatar a wayar masu da kawuna.

Wata makauniya ko nuna jin dadinta tayi saboda samun damar koyon ilimi a makarantar wanda tace ya kawo wa rayuwarta sauyi.

Ga karin bayani daga rahoton Haruna Mamman Bako.

Your browser doesn’t support HTML5

Yau Ce Ranar Nakasassu a Jamhuriyar Nijar - 3' 38"