Matasa su ne kashin bayan ci gaban kowace al’umma. Wannan ya sa majalisar dinkin duniya ta ware ranar 12 ga watan Agusta a kowace shekara a ke gudanar da bikin Ranar Matasa ta duniya domin nuna irin gudunmawar da matasa ke bayarwa wajen ci gaban al’umma da kuma kalubalen da suke fuskanta. Ana kuma gudanar da wannan rana domin wayar da kan matasa kan matsalolin da ke addabar duniya da suka hada da harkokin lafiya, adalci, aikin yi, harkokin siyasa da sauransu.
Taken ranar matasa na wannan shekarar shi ne: “Hadin kai tsakanin Jama’a: Kirkirar duniya ga dukkan shekaru”. Manufar ita ce fadada sakon cimma burin ci gaba mai dorewa ba tare da barin kowa a baya ba. Haka kuma za ta wayar da kan jama’a kan wasu abubuwan da ke kawo cikas ga hadin kan al’umma, musamman babanci sabili da shekaru, wadanda ke shafar matasa da manya, tare da yin illa ga al’umma baki daya.
Yawan shekaru ko karancin shekaru ga matasa lamari ne da yake da matukar muhimmanci a yau, kamar yadda rahoton Hukumar lafiya ta duniya (WHO) da aka kaddamar a Maris din shekarar 2021 ya nuna. Haka kuma matasa suke fuskantar wannan matsalar a bangarori daban-daban na rayuwa. Domin cimma wannan burin, mutane na bukatar a hadu a yi aiki tare da fahimtar juna.
Sarki Hashiru Dikeni matashin sarkin zangon Nmenmete dake yankin Accra, ya bayyana wa Muryar Amurka cewa shekaru ba su yi tasiri a harkokinsa na sarauta ba.
Sai dai Sadat Hamisu Barko, matashin dan siyasa, a nasa bangaren, ya ce ga al’adarmu ba a ja da manya, domin haka sai ana tauye wa matasa hakki a wurare da dama.
Maryam Mohammed Bawa, matashiyar ‘yar jarida ta nuna irin kalubalen da suke fuskanta a yayin da suke gudanar da aikinsu na jarida sabili da karancin shekaru. Ta ce, sabili da karancin shekarun ana tauye wa matasan ‘yan jarida damar ba da shawarwari yadda aikin zai tafi daidai.
Saurari cikakken rahoton Idris Abdullahi:
Your browser doesn’t support HTML5