Yau Ce Ranar Malamai Ta Majalisar Dinkin Duniya

Ban Ki-moon, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya

Ranar biyar ga watan Oktoban kowace shekara ce Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a takaice, ta ware a matsayin ranar malamai ta duniya.

Hukumar MDD dake kula da al'adu da inganta ilimi wato UNESCO ita ce take kebe ranar a duk fadin duniya a matsayin ranar malamai.

An kebe ranar ce domin tunawa da rawar da malamai ke takawa wajen bayar da ilimi da kuma cigaban al'ummar duniya.

Taken bikin na bana shi ne "Daraja Malamai da Kuma Daraja Matsayinsu A Duniya" abun da kuma tun ba yau ba malaman ke kuka da rashinsa. Ke nan an dade ba'a ganin darajar malamai ko ma aikin malunta a duniya.

Bikin na bana ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatoci da kungiyoyin sa kai ke faman ganin an samar da ilimi ga duk al'ummar duniya kafin nan da shekarar 2030 kamar yadda wani kudurin Majalisar Dinkin Duniya ya zartas.

Tambaya nan ita ce ina matsayin malami a Najeriya? Muhammad Sani wani tsohon malami a Najeriya yace gaskiya darajar malami a Najeriya ta tabarbare.

Sau tari ana ganin aikin malunta a Najeriya a matsayin wani aikin da bashi da daraja.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Yau Ce Ranar Malamai Ta Majalisar Dinkin Duniya - 2' 43"