Yau Ce Ranar Makamin Nukiliya Ta Duniya

Makamin nukiliya

Tun a shekarar 1946 ne Majalisar Dinkin Duniya, MDD ta tsayar da ranar Satumba 26 ta kowace shekara a matsayin ranar makamin nukiliya domin dakile yaduwar irin wannan makamin sanadiyar illar da ya yiwa kasar Japan lokacin da Amurka ta jefa mata makamin har sau biyu a yakin duniya na biyu lamarin da ya kawo karshen yakin.

A shekarar 1946 ce Majalisar Dinkin Duniya ta fito da dokar hana yaduwar makamin nukiliya a duniya wato bayan yakin duniya na biyu lokacin da Amurka ta sakawa kasar Japan makaman har sau biyu.

A sakonsa na bana babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres yana mai cewa akwai hanyoyi da dama da za'a bi wajen kawar da makaman nukiliya a duniya. Ya kira kasashen duniya su bada gudummawarsu wajen kawo karshen mallakar makaman.

Sai dai bana ana bikin ne a daidai lokacin da ake cacar baki tsakanin kasashen Koriya ta Arewa da Amurka. Cacar bakin nada nasaba da mallakar makamin nukiliya da Koriya ta Arewa ta hakikance a kai tare da yiwa juna barazanar kai hari. Sauran kasashen duniya dai sai hakuri suke bayarwa suna kiransu su kai zuciya nesa.

Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya, MDD sun nuna akwai makaman nukiliya 15,000 a kasashe daban daban musamman a kasashen da suka cigaba irinsu Amurka da Rasha da Ingila da Faransa da China da Indiya da Pakistan.

Shin ko menene makamin nukiliya? Dr. Babangida Jibrin Wushishi masanin kimiya yana mai cewa makamashi ne dake tsakatsakin atom. Atom kananan halartu ne dake cikin halitta. Ana hadasu da uranium. Ko a Najeriya ana iya samun uranium a jihohin Adamawa, Taraba, Bauchi, Kano da Cross Rivers.

A kan illar makamin, Malam Bashir Usman 'Yankuzo malami a Jami'ar Kimiya da Fasaha dake Minna yace nukiliya makami ne mai muni kwarai. Yana kone jiki da tarwatsa yanayi.

Amma kuma ana anfani da sinadiran makamin wajen ayyukan kimiya da fasaha da kuma magunguna a asibitoci. Ana kuma iya samun wutar lantarki.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Yau Ce Ranar Makamin Nukiliya Ta Duniya - 5' 07"