Kamar sauran takwarorinsu na sassan duniya daban-daban, ma’aikata a Najeriya da Janhuriyar Nijar sun bayyana korafe-korafensu da kuma farincikinsu a wurin bukin zagayowar ranar ma’aikata ta duniya baki daya.
Wakilinmu a Lagos Babangida Jibrin ya ce “a Najeriya wannan rana ta zo ne daidai lokacin da kungiyar kwadago ta gabatar ma gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke cika shekara guda da hawa bisa karagar mulki a wannan watan bukatar karin albashi na mafi karanci na Naira dubu 56 a maimakon Naira dubu 18 da gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ta amince da shi, wanda kuma har yanzu wasu gwamnatocin jahohi ke jan kafa wajen biyansa.”
Haka zalika, a jahohi irin Naija da sauran jahohin Najeriya kungiyoyin ma’aikatan sun bayyana korafe-korafensu. Amma gwamnatocin jahohin ma sun kare kansu.
A Janhuriyar Nijar ma ma’aikata sun bayyana korafe-korafensu. Daga Yamai Souley Mummuni Barma ya ruwaito wani babban kusa a kungiyar kwadago mai suna Malam Kaka Maitawayya na cewa ma’aikatan Nijar na cikin wani mawuyacin hali saboda karancin albashi da kuma jinkirin biya. Haka zalika, ma’aikata mata na fama da danniya kamar yadda Madam Chaibou Hajiya Hasana ta ce. A Damagaram kuwa, shugaban ma’aikata Mamman Galadima ya shaida ma wakiliyarmu Tamar Abari cewa su na bukatar hukumomi su dau matakan da su ka dace don inganta rayuwar ma’aikata.
Ga wakilan namu da rahotannin nasu:
Your browser doesn’t support HTML5