Yau Ce Ranar Ma'aikata ta Duniya

NLC Protest 2017

A yau ne ma’aikatan Najeriya su ka bi sahun sauran ma’aikata a kasashe 60 na Duniya, domin bukin Ranar Ma’aikata. Bukin na yau dai ya na zuwa ne kasa da wata guda da karin Albashi ga ma’aikatan kasar.

Kamar dai sauran ma’aikata a kasashe daban daban na Duniya, ma’aikata a Najeriya na fuskantar matsaloli da dama da suka hada da karancin albashi, rashin kulawa wajen aiki, da kuma rashin sanin makomar shi kanshi aikin.

Wasu 'yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu game da wannan rana, da cewar ko shakka babu su na farin ciki da wannan rana, kuma ya kamata gwamnati ta fito da wani tsari na kayyade farashin kayan masarufi a kasuwanni, maimakon karin albashi, domin hakan na bai wa 'yan kasuwa damar kara farashin kaya a kasuwanni.

Ita kuwa wata ma’aikaciya cewa ta yi, "duk ranar 1 ga watan Mayu muna wannan gangamin domin bukin ranar ma’aikata kamar haka, domin karawa ma’aikata kwarin gwiwa da kuma kwato masu 'yanci."

A bangare daya ma dai ma’aikata da ke kanfanoni masu zaman kansu na ganin karin albashin zai haifar da rufe wasu masana’antu, da kuma sallamar ma’aikatan daga aiki.

Kamar yadda kwamrad Musa Wushishi, na bangaren ma’aikatan fiton kaya a tashoshin jiragen sama dana ruwan kasa da ke Legas, ya shaida.

A bukin ranar ma’aikatan na yau dai ministan kwadago Dr. Chris Ngege, ya umarci gwamnatoci da kanfanoni masu zaman kansu, su hanzarta fara biyan albashin ba tare da bata lokaci ba. Taken bukin na bana dai shine shekaru 100 da gwagwarmayar neman yancin ma’aikata a duniya.

Wakilin Muryar Amurka, Babangida Jibril, ya aiko mana da karin bayani daga Legas.

Your browser doesn’t support HTML5

Ranar Ma'aikata Ta Duniya, Zamu Inganta Rayuwar Ma'aikata 2'10"