Duk da yake a Najeriya da ma wasu kasashe da dama an samu gagarumar nasara akan yaki da cutar amma har yanzu ana samun wasu kalilan da suke kamuwa da cutar.
Yayinda ake cigaba da kokarin kawar da cutar gaba daya daga doron duniya wadanda cutar ta riga ta yiwa illa a jihar Neja sun ce ba'a daukansu da mahimmanci ba duk da gagarumin taimakon da suke bayarwa a yaki da polio.
Malam Muhammad Awal shugaban kungiyar masu dauke da cutar a jihar Neja yace ko shi da yayi ilimin zamani kallon ukku kwabo ake yi masa balantana wadanda basu da ilimin.
Malam Awal yace yadda hukuma irin UNICEF ta kula da 'yancin yara a duniya haka ya kamata su dasuka nakasa ko ta sanadiyar polio a dinga kula dasu. Akwai abubuwa da yawa da suka kamata a yi masu da zasu kyautata rayuwarsu.
Jeringwanon da suka yi a Minna yana da matukar mahimmanci, musamman wajem fadakar da iyaye, inji jami'in yada labarai na kungiyar Yakubu Abdullahi. Yace duk wuraren da suka zagaya mutane sun taso sun shigesu. Irin jeringwanon na taimakawa wajen jawo hankalin jama'a da su amince da allurar rigakafi.
Dr Pati Shaikh Abdalla likitar sashen allurar rigakafi na ma'aikatar kiwon lafiya ta jihar Neja tace jeringwano na wayar da kai ne kuma suna kiran jama'a su basu goyon bayan cigaba da yaki da cutar.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5