A yau Lahadi 28 ga watan Yuli, itace ranar Ciwon Hanta da ake kira Hepatitis a turance, da hukumar hafiya ta duniya ta ware, Hukumar tana kira ga kasashe da su saka hannun jari cikin wadatattun yanyoyin jinya, wadanda za su iya rage yawan kamuwa da cutar, domin kubutar da miliyoyin mutane.
Cutar Hanta wato hepatitis rukunin B da C, kwayoyin cututtuka ne da ake yada su ta hanyar jini. Wadannan kwayoyin cuta guda biyu suna haifar da kansar hanta, sannan kuma wannan cuta ta kunshi kusan kashi 96 da ka iya kawo mutuwa.
Hukumar ta ce cutar Hanta wato hepatitis, rukunin B da C na shafar kimanin mutane miliyan 325 a duniya, kuma tana kashe kusan mutane miliyan 1.4 a kowace shekara. Shugaban Hukumar bangaren hepatitis, Marc Bulterys, ya ce, cutar hepatitis ta zama cuta ta biyu a duniya da ta fi yawan kasahe mutane bayan cutar tarin fuka.
Marc Bulterys, ya kara da cewa, "yawan masu mutuwa a sanadiyar cutar hepatitis, na karuwa a cikin shekaru 20 da suka gabata. Abin da ya fi muni, shine cutar hepatitis tana kashe mutune a cikin sauki. Daga cikin mutane miliyan 257 da muka kiyasta, suna rayuwa da kamuwa da cutar hepatitis rukunin B, kusan kashi daya cikin 10 ne aka gano, kuma kusan mutane miliyan 4.5 ne ke jinya."
Bulterys, ya ce daga cikin mutane miliyan 71 da ke rayuwa suna dauke da cutar hepatitis rukunin C, mutum daya cikin biyar ne kawai suke kamuwa da cutar kuma miliyan 5 ke jinya.
Binciken na hukumar ya gano cewa za a iya kawar da cutar hepatitis dake barazanar ga lafiyar jama'a a cikin kasashe 67, masu karamin karfi da kuma matsakaicin karfi zuwa 2030, kan farashin dala biliyan 6 a duk shekara, ko kuma kusan dala biliyan 60.
Wadannan kasashe suna da kashi 75 na yawan mutanen duniya. Hukumar ta ce za a rage sabbin kamuwa da cututtukan hepatitis da kashi 90 cikin 100, kuma za’a iya rage yawan mutuwar da kashi 65.
Lokacin da aka yi lissafi akan kowane mutum, Bulterys ya ce farashin magani yana da arha. Ya ce samar da magungunan na kwarai ne zai sa hakan yiwuwa. Sai ya kar da cewar, an dauki tsawon watanni uku ana yin maganin cutar hepatitis rukunin C a farashin $40 a Indiya, Pakistan da Eygpt, wadanda suka samar da nasu kwayoyin.
Ya shaidawa Muryar Amurka cewa, sauran kasashen duniya masu talauci na iya sayan magungunan a kan farashin dala $89 a shirin Majalisar Dinkin Duniya, bangaran cikigaba wato U.N. Development Programme da Gavi, da kungiyar allurar rigakafi ta duniya; amma ya kara da cewa farashin ya kasance mai girma a kasashe masu arziki.