Masu kada kuri’a a kasar Saliyo na garzayawa runfunan zabe a yau dinnan Laraba, don zaben sabon Shugaban kasa wanda su ke fatan zai jagoranci wannan kasa ta yammacin Afirka, ta yadda za ta fita daga yanayin tattalin arzikin da ya tabarbare bayan annobar Ebola ta 2014.
Mutane 16 ne ke takarar gadan Shugaba Ernest Bai Koroma mai baring ado, wanda ya kammala wa’adojinsa biyu masu tsawon shekaru biyar-biyar. ‘Yan takara biyu mafiya tashe su ne Samura Kamara na jam’iyyar All People’s Congress (APC) mai mulki, ta su Shugaba Koroma; da Julius Maada Bio, Shugaban jam’iyyar Sierra Leone People Party’s (SLPP). Jam’iyyun APC da SLPP sun taba jagorantar wannan karamar kasar daya bayan daya, tun bayan da ta samu ‘yancin kai daga Burtaniya a 1961.
To amma sabuwar jam’iyyar nan ta National Grand Coalition, wadda tsohon jami’in diflomasiyyar MDD Kandeh Yumkella ke jagoranta, ta ja hankalin matasa masu zabe, wadanda bas u goyon bayan APC da SLPP.
Kasancewar ‘yan takarar da yaw aka iya dada yiwuwar zuwa zagaye na biyu, muddun babu wanda ya zamu kashi 55% na kuru’un.