Yau An Tuna Da Yakin Duniya Na Biyu

  • Ibrahim Garba

Shugaban Amurka Donald Trump a hidimar tunawa da yakin duniya na biyu

Yayin da duniya ke cikin wani yanayi na zaman dardar saboda dalilai dabandaban, yau ake hidimar zagayowa ta 100, ta tunawa da wadanda su ka sadaukar da rayukansu a yakin duniya na daya.

A sa'a ta 11 ta yau Lahadi, 11 ga watan 11 -- wato shekaru 100 bayan yakin duniya na daya -- shugabannin kasashe 70 su ka taru a dandalin Arc de Triomple na kasar Faransa don tunawa da miliyoyin mutanen da su ka mutu a yakin.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugabannin akasarin kasashen da su ka tura sojoji ko sauran ma'aikata don goyon bayan yammacin duniya, sun hadu a kabarin da ake wa lakabi da "sojan da ba a san ko waye ba," wanda ke gaban dakalin dandalin, don kunna harshen wuta na har abada wanda akan kunna kowani dare a dandalin tunawa da 'yan mazan jiyan da aka rubuta kalmar: "Nan ne wani sojan Faransa ke kwance, wanda ya ba da ransa saboda kasarsa."

A jawabinsa, Macron ya tabo batun sadaukar da rayuka da aka yi shekaru da dama da su ka gabata, a yakin da aka shafe shekaru hudu ana yi a Turai. Ya ce "Alfahari da kasa akasin Kishin kasa ne."

Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Rasha Vladimir Putin su ne na karshe wajen isa wurin.