A yau alhamis hukumomin lafiya na Jihar Neja a arewacin Najeriya zasu kaddamar da aikin yin rigakafin kamuwa da cutar kyanda ko bakon dauro a duk fadin jihar.
Akwai jihohi da dama a kasar wadanda tuni su ma suka gudanar da irin wannan gangamin yin rigakafin wannan cuta mai yin illa sosai, har ma da janyo mutuwa, ga yara kanana.
Wakilin Muryar Amurka, Mustapha Nasiru Batsari, yace hukumomin lafiya na jihar sun bayyana fatar yin allurar rigakafin ga yara kimanin miliyan daya, wadanda suka kama daga masu watanni tara da haihuwa har zuwa ga masu shekaru biyar.
Kwamishinan ayyukan kiwon lafiya na Jihar Neja, Dr. Mustapha Jibril, yace gwamnati ta ware Naira miliyan 40 domin gudanar da wannan aikin rigakafi. Kwamishinan yace sun samu tallafi daga Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, da Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF da wasu cibiyoyin na kasa da kasa domin tabbatar da samun nasarar aikin.
Wani babban jami'in kiwon lafiya a jihar ta Neja, Dr. Salihu Bagoma, ya ce cutar kyanda ko bakon dauro, tana haddasa illoli da yawa, ciki har da rasa kunne, ko ido ko kuma gurguncewa.
Yace wannan rigakafin yana da tasiri sosai, domin yana bayar da kariya ga jikin yaro daga kwayoyin cutar.
An dauki matakan tsaro masu karfi sosai domin magance abubuwan da suka faru a baya na yin garkuwa da mutane, inda aka tura daruruwan sojoji da 'yan sandan kwantar da tarzoma.
Your browser doesn’t support HTML5