Yau alhamis shugaba Obama zai gabatar da jawabi akan sauye sauyen harkokin siyasa a gabas ta tsakiya

Shugaba Barack Obama na Amirka.

A yau alhamis idan Allah ya yarda, shugaba Barack Obama na Amirka zai yi wani baban jawabi akan sauye sauyen harkokin siyasa a gabas ta tsakiya da kuma arewacin Afrika. Fadar shugaban Amirka ta White House tace juyin juyan halin da suke faruwa a yankin dama ce ta tarihi na biyan bukatun begen al’ummar yankin, wadanda aka dade ana tauyewa yancin su ta siyasa da kuma damar samun bunkasar tattalin arziki.

A yau alhamis idan Allah ya yarda, shugaba Barack Obama na Amirka zai yi wani baban jawabi akan sauye sauyen harkokin siyasa a gabas ta tsakiya da kuma arewacin Afrika. Fadar shugaban Amirka ta White House tace juyin juyan halin da suke faruwa a yankin dama ce ta tarihi na biyan bukatun begen al’ummar yankin, wadanda aka dade ana tauyewa yancin su ta siyasa da kuma damar samun bunkasar tattalin arziki. Jawabin da shugaba Obama zai gabatar a ma’aikatar harkokin wajen Amirka, zai gabatar ne kwana daya bayan da Amirka ta azawa shugaban Syria takunkunmi a saboda yadda ake ketawa jama’a yancinsu a yayin mumunar sumamen da gwamnatin Syria ta kaiwa masu hamaiya. Fadar shugaban Amirka taki ta fadi, ko shugaba Obama zai bukaci shugaban Syria Bashar Al Assad yayi murabus, to amma ta lura da furucin da wani baban jami’in gwamnati Amirka yayi, da yace shugaba Assad yana da zabin jagorantar kasar sa zuwa ga tafarkin mulkin democradiya ko kuma yayi murabus.. Shugaba Obama zai gabatar da wannan jawabi ne a yayinda mumunar rikice rikice a Libya da Yamal da Syria da kuma a wasu wurare suka dakushe juyin juya hali mai farin jini da aka yi a kasashen Tunisia da Masar.