‘Yan Mali za su kada kuri’ar zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a yau dinnan Lahadi, yayin da su ke fargabar yiwuwar sake fuskantar harin ta’addanci, kamar yadda su ka firgita a zagayen farko na zaben makonni biyu da su ka gabata, lokacin da hare-haren ta’addanci su ka kawo cikas a runfunan zabe da dama a kasar.
Ba kawai tunanin yiwuwar hare-haren ta’addancin da ka iya shafar zaben ke damun ‘yan Mali ba, amma har ma da yadda zaben zai yi tasiri kan yakin da ake yi da kungiyoyin mayaka, wadanda ke da alaka da al-Ka’ida da ISIS.
Ministan Tsaron Mali, Tiena Coulibaly, ya gaya ma Muryar Amurka cewa tuni gwamnati ta dau matakin tabbatar da tsaro a fadin kasar a yayin da ake gudanar da zaben, kuma gwamnati ta himmantu ga yaki da kungiyoyin mayakan.