Yau Ake Cika Kwanaki 500 Da Sace Mata Da Yara A Garin N’GALEWA

Kungiyoyi masu zaman kansu da kare hakkin bil'adama a jamhuriyar Nijar, na kiran hukumomi da su kara kokari don ceto mata da yara kanana da aka sace, kimanin kwanaki 500 ke nan da suka gabata a kauye N'Galewa.

A yau 15 ga watan Nuwamba ake bukin cika kwanaki 500 da wasu ‘yan bindiga suka sace mata da yara kanana kimanin 39, a kauyen N’GALEWA dake yankin Fiffa, kungiyoyin kare hakkin jama’a sun bayyana damuwa.

Dan gane da abinda suka kira halin ko in kula da mahukuntan Nijer ke nunawa, wannan al’amari da suke ganin ya kai matsayin da shugaba Mahamadu Isuhu, da kansa ne ya kamata ya dauki matakin warwarewa.

A taron manema labaran da suka kira domin tunawa da wadanan mata da yara 39, na kauyen N’GALEWA shuwagabanin kungiyoyin fafitikar kare hakkin dan adam sun yi tunatarwa akan yanayin da wannan al’amari ya faru.

Mai magana da yawun kungiyar Kaka Touda Mamadou Goni, jigone a kungiyar AEC, shugaban kungiyar CONIDE mai kula da kare hakkin yara Moussa Sidikou, dake cikin wannan gwagwarmaya ta ceton mutanen N’GALEWA, na ganin rashin wani hobbasa daga wajen hukumomi tamkar take hakkin yara ne a kasar da saka hannu a yarjejeniyar kasa da kasa.

Kungiyoyin sun bayyana cewa, zasu ci gaba da gwagwarmaya ba fasawa, har zuwa lokacin da suka tabbatar wadanan mata da yara na N’GALEWA sun koma hannun iyayansu.

Your browser doesn’t support HTML5

Yau Ake Cika Kwanaki 500 Da Sace Mata Da Yara A Garin N’GALEWA 3'10"