Yaro Dan Shekaru 13 Ya Kashe Kansa a Gombe

  • Ibrahim Garba

Wasu yara a makaranta

A wani al'amari mai karkada hanji, wani yaro ya dan shekaru 13 da haihuwa ya yi abin ban tsaro da takaici, inda ya rataye kansa kamar yadda wasu baligai kan yi saboda damuwar rayuwa.

A wani al’amari mai ban takaici da kuma daure kai, wani yaro dan shekaru 13 da haihuwa ya rataye kansa a daki, inda aka samu gawarsa tsakanin karfe 12 zuwa 1 na rana.

Yaron dai dan wani babban jami’in dansanda ne mai suna Insifetto (Inspector) Abdu Manu. Mai magana da yawun Rundunar ‘Yansandan jahar Gombe DSP Mary Obe ba ta bayyana musabbabin daukar ransa da yaron ya yi ba. Ta ce har yanzu ana gudanar da bincike kan lamarin. To amma ta ce Rundunar ‘Yansanda ba ta tsare da mahaifin yaron saboda ba ta same shi da laifi ba a kalla zuwa yanzu.

DSP Mary ta ce yaron bai bar wata wasiyya ko rubutaccen sako ko bayani dangane da kashe kansa da ya yi ba. To saidai kungiyoyin rajin kare hakkin dan adam a Gombe sun ce su ma za su bi diddigin kashe kansa da yaron da bai gama mallakar hankalinsa ba ya yi. Ciyaman na ‘Civil Liberty Organization’ wanda kuma shi ne ciyaman na gamayyar kungiyoyin kare hakkin dan adam a Gombe, Muhammed Aliyu Wayer, ya ce su ma su na nan su na gudanar da nasu binciken.

Ga dai Abdulwahab Muhammad da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Yaro Dan Shekaru 13 Ya Kashe Kansa