Yaro Dan Shekaru 9 Zai Kammala Karatun Digiri

Laurent Simons

Laurent Simons, yaro ne dan shekaru 9 da haihuwa, bai banbanta da sauran yara masu wannan shekarun ba. Amma yana karatu a matakin digiri a fannin injiniyan lataroni “Electrical Engineering” a jami’ar fasaha ta ‘Eindhoven da ke kasar Belgiam.

A cikin wannan wata ake sa ran yaron zai kammala karatun nasa, wanda idan ya kammala zai zama yaro mafi karancin shekaru da ya kammala digiri a fadin duniya. Yaron ya kirkiro wata na’ura da za ta taimaka wa kwamfuta wajen ajiyar bayanai masu zurfi.

Yaron ya kara da cewar bayan kammala karatun shi yana sa ran ya cigaba da karatunsa har zuwa matakin digirin-digir-gir a fannin aikin likitanci, yaron dai ya kammala karantun sakandire a cikin shekara daya, a lokacin da aka gwada yadda kwakwalwar yaron ke aiki ta wuce tunanin kowa.

Laurent Simons

Yaron ya kammala karatun shi na jami’a wanda ya kamata ya dauke shi shekaru 3 ya kammala shi a cikin watannin 9. A shekarun baya an samu yaron da ya kammala karatun digiri din shi yana dan shekaru 10 da watannin 4, mai suna Michael Kearney cikin shekarar 1994.

Lauren, ya ce a duk lokacin da baya makaranta yakan fita yawo da dan kwikuyon shi, ko buga wasan bidiyo game kai harma da saka hotunan shi a shafin sa na Instagram. Idan ya kammala wannan karatun zai shiga cikin kundin tarihin duniya a matsayin yaro mafi karancin shekaru da ya kammala karatun digiri a fadin duniya.