Wata babbar kasuwar zamani wadda aka fi sani da Supermarket ta kasar Amurka mai suna ‘Chain Kroger Co’ a karon farko ta samar da dan-aiken cefanen zamani, wannan dan-aiken dai na’urace mai tafiya da kanta, da zata dinga kaima mutane cefanensu har gida a duk lokacin da suka yi siyayya ta shafin yanar gizo.
Kamfanin tare da hadin gwiwar wani kamfanin birnin Silicon Valley Nuro, sun fara aiki a karamar hukumar Scottsdale, dake jihar Arizona, don isar da sakon mutane gidajensu a duk lokacin da suka bukaci hakan.
Dan-aiken mai suna R1 na amfani da hanyoyin da mutane ke amfani da su wajen tafiya, babu wanda yake nunama dan-aiken hanya, domin kuwa an ingantashi da tsarin taswirar gari mai nuna mishi adireshi inda zai je don isar da sako.
A baya dai kamfanoni kamar su Walmart Inc, da Amazon, sun kashe makudan kudade don ganin sun samar da tsarin dan-aike mai cin gashin kansa, amma wannan kamfanin ya samar da tsarin da yafi nasu.
Domin kuwa wannan dan-aiken yana kai kowane irin sako gida, kama daga nama, alayyahu, tumatiri, albasa, lemu, ayaba da dai sauransu, fiye da na sauran kamfanonin da kawai ya kan kai sakon kayan da basu da mu'amala da ruwa.
Kamfanin Kroger yace ga duk mai bukata zai iya sayen duk abun da yake so, a kawo mishi a ranar ko washe gari akan kudi dallar Amurka $5.95 kimanin naira 20,000.