Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Larabawa da ma kungiyar tarayyar Turai suna kira ga bangarori masu yaki a Libya su kiyaye yarjejeniyar tsagaita wuta da ta fara aiki jiya Lahadi.
Shugabannin Rasha Vladmir Putin da na Turkiya Racep Tayyip Erdogan da suke marawa bangarori dabam daban baya, sun shafe makon suna kira da a tsaida yarjejeniya.
Ofishin MDD a Libya ya bukaci bangarori masu gaba da juna su mutunta shirin tsagaita wuta, kana su yi kokarin sasantawa.
Jakadun kungiyar Tarayyar Turai a Tripoli sun aike da sanawar hadin gwiwa suna rokon ‘yan Libya su ajiye makamai su sasanta muhimman batutuwan siyasa da na tattalin arziki da kuma na tsaro dake kawo yaki tsakaninsu.
Su ko kasashen kungiyar Larabawa, suna kara kaimi wurin kawo karshen yaki tsakanin abokan gaban na Libya, kana su kawar da duk wani tashin hankali su kuma amince da juna ta yadda zasu tabbatar da shirin tsagaita wuta mai dorewa.