Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Siriya Ta Tabbata

Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov sai kuma wakilin MDD na musamman akan Siriya Staffan de Mistura a hannun hagu yana magana dasu

Tsagaita wutar rikicin Syria da Amurka da Russia suka shirya, ya nuna alamun karbuwa a duk fadin kasar da yaki ya daidaita.

Amma rarraba kayan agaji a garuruwan da sojojin gwamnati suke rike dasu shine mafi muhimmanci. Daya daga cikin abubuwan da aka tsaya akai shine shiryawa da gwamnatin Siriya dangane da irin taimakon da za’a akai birnin Aleppo, Birnin da ya fi kowane Birnin fama da bala’in yaaki na fiye da shekaru biyar.

Masu bada agajin gaggawa sun ce suna jiran tabbacin an share masu hanya ba wai daga bangaren Shugaba Al-Bashir kadai ba a’a harma da sauran bangarorin da ake fafatawa dasu.

Staffan de Mistura Jami’in na musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Syria ya bayyanawa ‘yan jaridu a Geneva cewa tashe tsahen hankula sun ragu matuka sannan babu hare haren jiragen saman yaki kwatakwata.