‘Yar Shugaban kasar Amurka Donald Trump kuma mai ba da shawarwari a fadar White House, Ivanka, ta ziyarci kasar Ivory Coast a ziyarar aiki ta kwanaki hudu da take yi domin inganta tattalin arzikin mata a yankin yammacin Afrika.
WASHINGTON D.C. —
Da ta ke jawabi a Cayat, a wata gonar koko da ke wajen Adzope a jiya Laraba, Ivanka Trump ta sanar da cewa cibiyar raya kasashe ta duniya USAID a takaice, da wasu kamfanoni masu zaman kansu za sun hade da alkawarin dalar Amurka miliyan biyu ga horkokin masu sana’ar koko a Ivory Coast.
Duk da yake a Ivory Coast, Shugaba Trump ya na shirrin halartar taron bankin duniya.
Ita Ivanka din, wacce ta kasance mai ba da shawara ga mahaifinta kan karfafa tattalin arziki, ta fara tafiya zuwa yankin tare da ziyararta a babban birnin Habasha na Addis Ababa ranar Lahadi da ta gabata, inda ta sanar da shirin gwamnatin Amurka na miliyoyin dalar Amurka don tallafa wa 'yan kasuwa mata.