An haifi Roxy a nan Amurka amma ta yi girma tsakanin Najeriya da Amurka. Inda ta rika zuwa Najeriya tana zama da kakanninta, kafin da ta kai shiga sakandare ta dawo da mahaifiyarta suka zauna a birnin Bowie.
Roxy wata matashiya ce mai kyakkyawar fata, wadda take aiki a fannin fasaha, wadda ta girma tsakanin Najeriya da Amurka.
A cikin hirarta da Grace Alheri Abdu, Roxy tace ta zauna na lokaci mai tsawo da kakanninta a kauyen Arachuku. Ta kuma yi cudanya sosai da dangi a karkararsu a Najeriya da kuma wadanda suke a biranen Lagos da kuma Abuja. Wannan ya sa ta koyi abubuwa da dama.
Mahaifiyarta tayi aiki tukuru domin ta sami kudin da zata sa ti makaranta mai zaman kanta, bayan haka a shekara ta dubu da dari tara da casa’in da tara suka koma birnin Bowie da mijin mahaifiyarta wanda yake a matsayin uba a gareta amma tace mutumin bashi da kirki ko kadan.
Bayan ta kamala makarantar sakandare ta shiga jami’a domin karanta fannin aikin jinya, tana kokarin bin gurbin mahaifiyarta, da nufin fahimtar matsalolin lafiya da suka shafi tsirarru, musamman Amurkawa bakaken fata, amma daga baya ta gane cewa, tafi sha’awar fannin fasaha. Kasancewa ta zauna a Najeriya na lokaci mai tsawo, ta faminci kalubalar da Najeriya ke fuskanta a wannan fannin, sabili ke nan ta fara aiki da kamfanin sadarwa na Microsoft.
Aiki da kamfanin Microsoft ya sa ta fara sha’awar abainda ya shafi al’umma da gwaggwarmaya kan abinda ya shafe su, saboda haka da ta kara girma, sai mutane suka rika bata shawara cewa ta tsaya takarar neman wani mukami. Yadda aka yi ke nan ta kai ga tsayawa takara aka zabe ta a majalisar Birnin Bowie.
Shekaru biyu bayanda Roxy ta kamala jami’a ta ziyarci makarantar da ta yi sakandare ta kuma zagaya birnin Bowie sai ta lura abubuwa sun sake sosai ba kamar yadda suke a da ba. Komi ya koma baya, ba kamar yadda yake lokacin da take girma ba. Inda kowa yake kula da jin dadi da kuma ci gaban kowa. Sai kace, an kaucewa ainihin abinda aka san birnin da shi , inda ake taimakwa kananan masana’antu da kula da muhalli, da kawata birnin. Sai kace komi ya koma da baya.
Ganin yadda ta damu ainun da ci gaban birnin yasa wata rana mai bata shawara ya tambaye ta menene yasa ba zata tsaya takara ba?
Duk da yake lokaci yana nema ya kure, Roxy ta cika takardar tsayawa takara ana saura watanni biyu a yi zabe, ta kuma zaga tayi yakin neman zabe gida gida tare da taimakon magoya bayanta, ta kuma dace aka zabe duk da yake ita ce mafi kankantar shekaru, kuma ba ‘yar siyasa ba, ta doke saurana mutane uku da suka yi takara da su ta lashe zabe.
Roxy Ndebumadu ‘yar shekaru ishirin da shida da haihuwa ta kasance mace mafi kankantar shekaru da aka taba zaba a matsayin memba a majalisar gudanarwa ta birnin Bowie. Za a rantsar da ita ranar goma sha takwas ga watan Nuwamba.