Yanzu ‘yan jam’iyyar PDP, sun canja salon kamfe

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Yanzu ‘yan jam’iyyar PDP, sun canja salon kamfe, kama daga shugaban jam’iyyar ta PDP, Ahmed Mua’zu, zuwa sauran wadanda sukayi nasarar samu tikitin takara, a PDP, sun sauya salon kamfe da Allah ne yasan gaibu. Maimakon da can yadda suke nunawa ba wanda ya isa ya kayar dasu zabe, ko akidar nan ta amutu ko ayi rai.

Bayan ga Gwamnatin tarayya da PDP, ke jan rakama, ita cema ke jagorantar majalisar wakilai da dattawa, in aka cire kwananan da kakakin majalisar wakilai Aminu Tambuwal, ya koma adawa.

A nashi bangaren madugun adawa janar Muhamadu Buhari, ya sake salon ma’amala da mutane, inda a yanzu ya kan kaiwa sauran abokan tafiyarsa ziyara, ya yiwa saura jama’a murmushi awuraren taro, harma da nuna karfin gwiwar cewa canji Gwamnati mai yiwuwa.

Your browser doesn’t support HTML5

sake salon Kamfe - 3'54"