Yanzu Muna Kan Gudanar Da Sabon Fim Mai Lakabin Bilkisu- Inji Nura Sharif

Nura Sharif

A yanzu masu shirya fina-finai sun fi maida hankali wajen fitar da fina-finan talabijiN ko akan tashar youtube domin abinda zamani ya zo da shi Kenan duk kuwa da cewar shafin youtube shafi ne da ke tattare da kalubale da dama inji Nura Sharif Ibrahim.

Nura Sharif, dai darakta ne kuma furodusa da mai rubuta fim ne, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da wakiliyar DandalinVOA inda ya ce harkar fim harka ce ta kirkira domin samun cigaba a masana’antar

ya ce idan aka duba cigaban zamani bayan mai fim ya kai fim dinsa gidan sinima ko gidan talabijin, wuri na gaba da masu shirya fim ke kaiwa shine sanya fim a shafin youtube ko da yake shafin youtube na dauke da kalubale ganin cewar kafa ce da ba’a tantance ta kuma za’a iya sanya duk abinda aka ga dama.

Mal Nura ya kara da cewa fannin youtube na dauke na cigaba a lokaci guda muka yana tattare da kalubale da dama, inda mai fim zai iya saka fim dinsa a youtube ba tare da an tace fim din ba.

Sanin dukkanin fanonin harkar fim ne ke baiwa mutum damar lakantar dukkanin fanonin masana’antar tare da warware matsalolin da ke ciwa mutue tuwo a kwarya.

Ya ce a yanzu suna gudanar da fim din Bilkisu mai nisan zango, kuma fim ne da ya saba da fina-finan da aka saba kallon, inda fim din ya kunshi labari na Bilkisu tare da nuna irin gwagwarmayar da ta fuskanta tun daga shiga makarantar firamare har jami’a da kuma samun aikinta a matsayinta na mace.

Your browser doesn’t support HTML5

Yanzu Muna Kan Gudanar Da Sabon Fim Mai Lakabin Bilkisu- Inji Nura Sharif