Gwamnatin jihar Bauchi ta kirkiro da dokoki da zai hukunta masu aikata munanan laifuka da suka hada da satar mutane, fyade, luwadi da madigo da kuma satar dabbobi.
WASHINGTON, DC —
Dokar zata daure mutun tsawon rai da rai idan aka sameshi da laifin aikata fyade sauran hukince hukuncen sun tanadi dauri a gidan yari kama daga shekaru ashirin da biyar (25) zuwa talatin (30).
Sai dai kuma an kirkiro da dokar da zai samar da ayyukan kula da lafiya da kyuatatawa mutanen da suka gamu da hatsari akan hanya kyauta a Asibitocin gwamnati dake fadin jihar.
Gwamnar jihar Barrister Muhammad Abdullahi, shine ya sanya hannu akan dokokin domin fara aiki dasu.
Babban mai gabatar da kara na gwamnati, kuma kwamishinan shara’a na jihar Bauchi, Barrister Yakubu Ibrahim, shine ya karanto dokokin kamar haka.
Your browser doesn’t support HTML5